Da yake tabbatar da hakan a jiya Talata a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, Shugaba Buhari, ya alkawarta tura wani kudurin doka zuwa majalissar dokokin kasar, wanda zai tabbatar da aiwatar da karin albashin, bayan da ya karbi rahoton kwamiti mai bangarori uku na masu ruwa da tsaki, wanda ya nazarci batun karin albashin.
Shugaban ya ce gwamnatinsa na mai da hankali matuka ga batun karin albashin, yana mai kira ga ma'aikata 'yan kwadago, da kada su bari a yi amfani da su wajen cimma burin siyasa.
Gabanin hakan dai kungiyoyin 'yan kwadago a Najeriyar sun shirya shiga yajin aiki na sai baba ta gani tun daga jiya Talata, suna masu zargin gwamnatin kasar da gaza cika alkawuran da ta yi a baya, na karawa ma'aikatan kasar albashi kamar yadda doka ta tanada. (Saminu Hassan)