in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin: Tattalin arzikin Sin na cikin yanayi mai karko
2018-10-25 11:19:03 cri

Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya halarci taron wakilan babbar kungiyar ma'aikata ta kasar Sin, a jiya Laraba, inda ya yi bayani kan yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki.

A cewar firaministan, kasar Sin na ci gaba da kokarin zurfafa gyare-gyaren cikin gida gami da kara bude kofarta ga kasashen waje. Duk da cewa akwai wasu matsaloli, amma kasar ta yi kokarin tinkararsu, tare da sanya tattalin arzikin kasar ya zama cikin wani yanayi mai karko. Idan an dubi alkaluman da aka samu game da karuwar tattalin arzikin kasar tun daga watan Janairu har zuwa watan Satumba na bana, za a ga saurin karuwar yana kan gaba a duniya. Haka zalika, tsakanin wannan lokaci, an samu damar samar da karin guraben aikin yi da suka kai miliyan 11.07, yayin da a kusan a kowace rana, ana samun budewar sabbin kamfanoni fiye da dubu 18 a kasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China