in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin zai gana da jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa
2018-10-30 19:10:18 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai gana da jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa guda shida, a ranar 6 ga watan Nuwamba dake tafe a nan birnin Beijing.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Lu Kang, ya ce Li Keqiang zai tattauna da jami'an ne game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, da batun kare harkokin cinikayya tsakanin sassa daban daban, da kuma sauye sauye da Sin ke gudanarwa a fannin tattalin arziki, da kara bude kofa ga kasashen waje.

Jami'an dai sun hada da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, da babbar daraktar asusun bada lamuni na duniya Christine Lagarde, da babban daraktan kungiyar cinikakka ta kasa da kasa ko WTO Roberto Azevedo. Sauran su ne, babban sakaraten kungiyar bunkasa hadin kan tattalin arziki da samar da ci gaba Angel Gurria, da shugaban hukumar samar da daidaito a fannin hada hadar cinikayya Mark Carney, da kuma mataimakiyar babban daraktan kungiyar kwadago ta kasa da kasa Deborah Greenfield.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China