Li Keqiang ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, inda ya ce ya kamata kasar Sin da EU su ci gaba da tuntubar juna.
Ya ce ci gaba da inganta alakar Kasar Sin da Tarayyar Turai ba bukatunsa kadai zai kai ga cimmawa ba, har ma da taimakawa wajen inganta zaman lafiya da ci gaban duniya. (Fa'iza Mustapha)