in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada niyya da imanin kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje
2018-11-07 21:17:15 cri

A kwanan baya, a lokacin da yake rangadin aiki a birnin Shanghai, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne a mayar da tunani game da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, a kuma dauki kwararan matakan aiwatar da manufofin da kwamitin kolin jam'iyyar ya tsara, domin tabbatar da tsayawa imani, da niyyar kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, sannan bisa ka'idar neman ci gaba ba tare da tangarda ba, da aiwatar da sabon tunanin neman ci gaba, da kuma kara yin kwaskwarima kan sana'o'in masana'antu bisa bukatun da ake da su a kasuwa, ta yadda za a iya kafa wani tsarin tattalin arzikin zamani, da kuma hanzarta samar da karfin gogayya mafi muhimmanci ga birnin Shanghai, ta yadda zai iya kara samar da hidima ga ayyukan kwaskwarima da ake yi a sauran yankunan kasar. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China