Ana sa ran za a yi gwajin juriyar jirgin ta fuskar makamashin da yake amfani da shi, da sauran kayan ayyukan sa fannin na'urori da dai sauran su.
An kammala aikin kera jirgin ne tun fara aiki a watan Afrilun shekarar bara, an kuma kammala gwaje gwajen kayan aikinsa, da na tsarin gudanar da ayyukansa. An kuma gama duk wasu ayyuka da suka shafi yadda za a rika turke jirgin, duka dai da nufin tabbatar da nasarar gwajin da za a yi da shi a kan teku. (Saminu Hassan)