"Za mu mayar da martani ba wai kawai saboda janyewar Washington daga yarjejeniyar ba, sai dai saboda irin matakan da Amurka ta dauka a aikace saboda tana da ikon da za ta aikata abin da take so," in ji Konstantin Kosachev, shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar dokokin kasar Rasha, ya fada a lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta Rossiya 24.
Ya kara da cewa, "kamar yadda shugaban kasarmu ya fada, Rasha tana da dukkan kwarewar sojoji a wannan fanni, martanin da za mu mayar cikin hanzari ne."
A ranar Asabar ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa kasarsa za ta fice daga yarjejeniyar INF inda ya zargi Rasha da saba yarjejeniyar da suka cimma.
Tun da farko a jiya Lahadi, jami'an kasar Rasha da dama sun yi gargadin Amurka game da ficewa daga yarjejeniyar, sun bayyana cewa daukar wannan mataki al'amari ne mai matukar hadari.
A shekarar 1987 aka kulla yarjejeniyar ta INF tsakanin tarayyar Soviet da kasar Amurka dangane da kawar da makaman nukiliya masu cin gajere da matsakaicin zango. (Ahmad Fagam)