in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojojin Isra'ila ta yi watsi da zargin Rasha na harbo jirgin samanta a Syria.
2018-09-24 13:24:46 cri
Rundunar sojan Isra'ila ta yi watsi da sakamakon binciken da ma'aikatar harkokin tsaron Rasha ta gabatar, inda ta zargi kasar Isra'ila da hannu kai tsaye a harbo jirgin saman Rasha a kasar Syria.

Mahukuntan Isra'ila sun fitar da wata sanarwa 'yan sa'o'i bayan da ma'aikatar tsaron kasar Rashar ta gabatar da sakamakon binciken game da lamarin da ya faru a Latakia ranar Litinin din da ta gabata, inda take zargin sojojin Isra'ila da mummunan sakaci.

An harbo jirgin saman mai dauke da mutane 15 ne da wani makami mai linzami na kasar Syria bisa kuskure, lokacin da sojojin Isra'ila ke kai hari ta sama kan lardin Latakia na kasar Syria.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Rasha Konashenkov ya shaidawa manema labarai cewa, suna zargin sojojin saman Isra'ila da ma wadanda ke da hannu wajen aikata wannan danyen aiki kan jirgin saman kasar ta Rasha.

Sai dai dakarun tsaron Isra'ila sun fitar da sanarwa, suna masu bayyana cewa, sojojin saman kasar ba su fake a bayan wani jirgi ba, kuma jiragen saman Isra'ila suna sararin samaniyar kasar a lokacin da aka harbo jirgin saman Rasha.

Dakarun Isra'ila sun ce ba za su daina kai hare-haren da suke yi kan sansanonin Iran dake Syria ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China