in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta bankado makarkashiyar kai harin ta'addanci sau ashirin a bara
2018-01-09 11:02:17 cri
Ministan kula da harkokin cikin gidan kasar Faransa, Gerard Collomb ya ce, a shekarar da ta gabata Faransa ta bankado makarkashiyar kai harin ta'addanci har sau ashirin a sassan kasar.

Rahoto daga jaridar Le Progrès ta Faransa ya ruwaito Mista Collomb na jaddada cewa, a halin yanzu babu wani wuri wanda ke da cikakken tsaro dari bisa dari a kasar, shi ya sa ya zama dole a yi hattara ga yiwuwar farmakin ta'addanci a ko'ina.

Rahotanni sun ce, a karshen watan Disambar bara, a biranen Paris da Lyon, hukumomin tsaron Faransa sun kame wata matashiya mai shekaru 19 da haihuwa gami da wani matashi mai shekaru 21 da haihuwa, wadanda dukkansu suka yi yunkurin kai harin ta'addanci.

Daga aukuwar harin ta'addanci a mujallar Charlie Hebdo ta Faransa a watan Janairun shekara ta 2015, ya zuwa yanzu, kasar na fuskantar babban kalubale a fannin tsaro. Don haka, gwamnatin Faransa na daukar wasu tsauraran matakai na yaki da ayyukan ta'addanci, ciki har da kara jibge 'yan sanda masu sintiri, da katse hanyoyin da 'yan ta'adda suke bi wajen tattaro kudade.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China