Shugaba Rouhani ya bayyana haka ne jiya Lahadi a Jami'ar Tehran.
Gidan talabijin na Press ya ruwaito shugaban na cewa, takunkuman da za su fara aiki ranar 4 ga watan Nuwamba ba za su yi tasiri kan harkokin kasar ba, sai dai ya ce manufar matsin lambar ta Amurka ita ce neman sauya gwamnatin Iran.
A ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, inda kuma ya lashi takobin sake kakabawa kasar takunkumai mafi tsauri da aka taba sanya mata.
Zagaye na farko na takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran a ranar 7 ga watan Agusta, ya haramtawa Iran din sayen takardar kudin dala da karafa, wanda wani bangare ne na yunkurin yanke kasar daga tsarin hada-hadar kudi ta duniya.
Zagaye na biyu na takunkuma kuwa, sun shafi man fetur da isakar gas da Iran din ke fitarwa, wadanda za su fara aiki a ranar 4 ga watan Nuwamba mai zuwa. (Fa'iza Mustapha)