Wata sanarwa ta hukumar ta fitar a jiya Lahadi, ta bayyana cewa, 'yan gudun hijira 44 daga kasashen Syria,da Sudan da Palasdinu sun isa kasar Italiya lami lafiya, a wani bangare na shirin hukumar game da sake tsugunar da 'yan gudun hijira.
Shirin raya arewacin Afirka wanda hukumar tarayyar turai tare da gamayyar kasashen turai 14 gami da kasar Italiya wadda ke jagorantar shirin ne suke aiwatar da shirin sake tsugunar da 'yan gudun hijirar kasar ta Libya .
Kasar Libya dai ta kasance zangon da bakin haure ke amfani da ita wajen shiga kasashen turai ta hanyar tsallaka tekun Bahar Rum, sakamakon matsalar tsaro da kasar ke fama da ita, biyo bayan boren shekarar 2011 wanda ya kai ga kifar da tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi.
Dubban bakin haure ne dai ke makare a wuraren tsugunarsu wadanda da aka ceto a teku ko hukumomin tsaron kasar suka damke. (Ibrahim)