Babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya sanar da hakan jiya Alhamis, ya ce, sabbin matakan samar da hadin kai da sasantawa da gwamnatin firaministan Habasha Abiy Ahmed ta dauka, sun taimaka matuka, kana fadan kabilanci ya haifar wa sabuwar gwamnatin kalubale.
Guterres ya ce, kimanin mutane miliyan 1 ne fadan ya raba da matsugunansu, wadanda ke bukatar taimakon gaggawa. Sai dai ana fuskantar wahalar shiga wasu wuraren saboda shigowar damina. (Ibrahim)