in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya jaddada takunkumi ga wasu sassa na kasar Mali
2018-08-31 11:13:38 cri
Kwamitin tsaron MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2432, wanda ya tanaji sanya takunkumi ga wasu sassa na kasar Mali. Takunkumin dai ya kunshi daskaras da dukiyoyi, da kuma hana wasu mutane 'yan kasar ikon tafiye tafiye, sakamakon hannu da suke da shi a tashe tashen hankula, da gurgunta zaman lafiya, tare da yin kafar ungulu ga tsaron kasa. Kaza lika an amince da ayyukan majalissar kwararru, wadda ke bibiyar tasirin matakan da ake dauka a kasar.

An dai amince da kudurin mai lamba 2432 ne, biyowa bayan kuduri mai lamba 2374 na shekarar da ta gabata. Sabon kudurin zai yi aiki ne har zuwa ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2019. Kana shi ma aikin kwamitin kwararrun zai ci gaba da gudana, ya zuwa ranar 30 ga watan Satumbar shekarar ta 2019.

Kwamitin tsaron MDDr na fatan karbar rahoton tsakiyar aiki daga kwamitin, nan da ranar 28 ga watan Fabarairun shekarar 2019. Da kuma rahoton karshe a ranar 15 ga watan Agustan shekarar ta 2019, baya ga kananan rahotanni tsakanin wadannan lokuta, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Mambobin kwamitin sun amince babban magatakardar MDDr ya dauki matakan gaggawa, don tabbatar da sake kafa majalissar kwararru, da hadin gwiwar kwamitin, ta yadda za a tsara, tare da zartas da ayyukan mambobin kwamitin na yanzu yadda ya kamata.

Duk da cewa kuduri mai lamba ta 2374, ya tanaji babban magatakardar MDDr tare da 'yan kwamitin, da wasu kwararru 5 sun gana da juna, 4 daga cikin mambobin majalissar kwararrun ne kadai aka samu damar kaddamarwa, bayan da kasar Rasha ta nuna adawa da nadin mamba na 5 a majalissar kwararrun.

A ranar 5 ga watan Satumban shekarar 2017 ne aka amince da kaddamar da kuduri mai lamba 2374, wanda ya tanaji takunkumai ga wasu sassa na kasar Mali.

A wancan lokaci an kafa kwamitin da zai lura da sanyawa sassan kasar ta Mali takunkumai, aka kuma bukaci babban magatakardar MDD da ya kafa majalissar kwararru, domin tallafawa ayyukan kwamitin wanda wa'adin aikin sa zai kare cikin watanni 13. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China