in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi tir da harin da aka kai wa jami'an wanzar da zaman lafiya a CAR
2018-06-12 09:23:42 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da wasu masu dauke da amkamai suka kai wa jami'an shirin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

An farwa jami'an ne shekaranjiya, a lokacin da suke aikin sintiri, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda da raunatar wani.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Antonio Guterres, ya ce kashe jami'in dan kasar Burundi, ya kawo adadin jami'an wanzar da zaman lafiya da aka kashe a kasar tun daga watan Junairun bana zuwa 5, inda aka kai hare-hare biyu cikin mako guda.

Sakatare Janar din ya kuma jadadda cikakken goyon bayansa ga shirin dake aiki a Jamhriyar Afrika ta tsakiya wato MINUSCA, a kokarin da yake na kare fararen hula da wanzar da zaman lafiya a kasar.

Ya kuma tunatarwa maharan cewa, hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD, ka iya zama laifin yaki, kuma za a iya kakabawa wadanda ke da hannu takunkumi, yana mai bukatar hukumomi a kasar su gudanar da bincike domin gano masu laifin, ta yadda za a hukunta su. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China