in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya nemi taimakon kasa da kasa game da batun cutar Ebola a DRC
2018-10-31 09:55:02 cri
Taron kwamitin sulhun MDD da ya gudana a jiya Talata ya cimma matsayar neman tallafin kasa da kasa game da barkewar annobar cutar Ebola a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC wanda aka samu na baya bayan nan.

A kuduri mai lamba 2439, kwamitin ya nanata muhimmancin ci gaba da ba da tallafin kasa da kasa, domin kawo karshen annobar cutar ta Ebola mai saurin kisa.

Haka zalika, kwamitin ya karfafawa DRC gwiwa, da hukumar lafiya ta duniya WHO da sauran kungiyoyi masu bada agaji wajen yaki da cutar Ebolar da su ci gaba da inganta ayyukansu da kuma tabbatar da alkinta alkaluman da aka samu na bullar cutar ta Ebola yadda ya kamata.

Kwamitin na MDD ya bayyana damuwa game da matsalar tabarbarewar tsaro wanda ke kawo cikas a shirin yaki da kwayar cutar Ebola a DRC.

Sannan ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su mutunta dokokin jin kai bil adama na kasa da kasa, da dokokin kare hakkin bil adama na kasa wanda hakan zai bada damar shigar da kayayyakin jin kai da jami'an kiwon lafiya tare da kayayyakin aikinsu domin tabbatar da ba su kariyar da ta kamata bisa dokokin na kasa kasa.

An samu barkewar cutar Ebola na baya bayan nan ne a arewacin lardin Kivu da Ituri a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo a watan Augasta. A cewar hukumar WHO, ya zuwa ranar 23 ga watan Oktoba mutane 212 ne aka yi amana sun kamu da cutar kana wasu mutanen 35 kuma ake tsammanin sun kama da cutar ta Ebola. Daga cikin mutane 159 da aka ba da rahoton sun mutu, mutane 124 an tabbatar da cewa cututtukan dake da nasaba da Ebola ne suka hallakasu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China