in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Ali Bango Ondinba na Gabon yana kara samun koshin lafiya
2018-11-12 10:04:06 cri
Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Gabon Ike Ngouomi, ya bayyana cewa, shugaba Ali Bango Ondinga na kasar wanda ke jinya tun ranar 24 ga watan Oktoba a wani asibitin dake kasar Saudiya sakamakon kasala da hajijiya, yana kara samun sauki.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kakakin fadar shugaban kasar ya ce shugaba Ali Bango yana kara samun lafiya matuka.

A ranar 24 ga watan Oktoba ne dai shugaban ya fara jin kasala da hajijiya a lokacin da yake zaune a wani Otel a birnin Riyadh na kasar Saudiya. Bayan da likitansa ya duba shi ne kuma aka garzaya da shi asibitin sarki Faysal dake birnin na Riyadh domin a kara duba lafiyarsa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China