Hukumomin kasar ta Gabon sun bayyana cewa, ya zama tilas su karfafa ayyukan jami'an kiwon lafiyar kasar da masana yaduwar kwayoyin cutaka don tsananta bincike a kan iyakokin kasar da filayen jiragen sama.
A cewar hukumar ta WHO, kasashen jamhuriyar Kongo, da jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, da kuma Gabon, suna daga cikin jerin kasashen dake cikin hadarin kamuwa da cutar. Sai dai kawo yanzu ba'a samu rahoton bullar cutar ta Ebola ba a kasar Gabon.
Domin daukar matakan kariya, hukumomin kasar Gabon sun yanke shawarar daukar matakai da suka hada da dakatar da zirga zirgar jiragen sama dana ruwa tsakaninta da kasashen da aka samu bullar cutar, sannan zata dakatar da bada takardun izinin shiga kasar ta Gabon ga fasinjoji da suka fito daga kasashen da aka samu rahoton bazuwar cutar.(Ahmad Fagam)