in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake nada Issoze-Ngondet a matsayin firaministan kasar Gabon
2018-05-04 09:46:44 cri
A jiya Alhamis ne aka sake nada Emmanuel Issoze-Ngondet a matsayin firaministan kasar Gabon, bayan ya sauka daga wannan mukami a ranar Talata.

Da yake karanta wata sanarwar shugaba, babban sakatare a fadar shugaban kasa Jean Yves Teal, ya ce, shugaba Ali Bongo Ondimba na Gabon ya umarci Issoze-Ngondet da ya kafa sabuwar gwamnati.

A ranar 1 ga watan Mayun wannan shekara ce dai Isso-Ngondet ya yi murabus, sakamakon wata shawara da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yanke na rushe majalisar dokokin kasar, saboda karewar wa'adinta na shekaru biyu, don a kuma bukatar ganin an shirya zabe a kan lokaci.

Kotun dai ta rushe gwamnatin ne saboda ta gaza shirya zabukan majalisar dokoki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China