Ali Bongo ya ce, jama'ar Gabon da Sin na da dadadden zumunci, kana, kasashen biyu na da ra'ayoyi kusan iri daya kan wasu batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Gabon ta jinjinawa kasar Sin saboda muhimmiyar rawar da take takawa a duk fadin duniya baki daya.
Gabon na son zurfafa hadin-gwiwa da mu'amala tare da kasar Sin, musamman a fannin tsaro, da karfafa alaka tsakanin rundunonin sojansu, a wani kokari na tinkarar kalubalen tsaro kafada da kafada.
Shi ma a nasa bangaren, Mista Chang Wanquan ya ce, shugaba Xi Jinping da Ali Bongo sun daga matsayin dangantakar kasashensu har zuwa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa daga dukkanin fannoni, abun da ya kafa alkibla ga makomar dangantakarsu. A 'yan shekarun nan, rundunonin sojan kasashen Sin da Gabon na kara yin mu'amala da hadin-gwiwa. Kasar Sin na fatan yin kokari tare da Gabon, wajen fadada hadin-gwiwarsu a fannonin da suka shafi horon soja, da kiwon lafiya ta fuskar soja da dai sauransu.(Murtala)