in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Gabon ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2018-01-16 09:53:55 cri

Jiya Litinin ne, shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadar shugaban kasa dake binin Libreville, wato babban birnin kasar.

A yayin ganawar tasu, shugaba Bongo ya ce, yana fatan kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya da kuma baiwa kasarsa taimako a fannin neman bunkasuwa, da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.

Ya kara da cewa, kasar Gabon ta yaba matuka da manufofin diflomasiyyar kasar Sin a fannin hadin gwiwa, mutunta juna da kuma neman daidaito a tsakanin kasa da kasa. A don haka, yana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka. Yayin da shi kuma zai ci gaba da martaba manufar "kasar Sin daya tak a duniya" domin kiyaye dunkulewar kasar Sin baki daya da kare 'yancin kasar kan batun tekun Kuduncin kasar ta Sin .

Haka kuma, ya ce, kasar Gabon za ta dukufa wajen aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma ba da gudummawa ga kasar Sin da ta samu nasarar gudanar da taron koli na dandalin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka na FOCAC da za a yi a birnin Beijing a wannan shekara.

A nasa bangare, Wang Yi ya nuna cewa, kasar Sin tana son habaka hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin da kasar Gabon ta fi kwarewa, haka kuma, kasar Sin tana goyon bayan kasar Gabon da ta ba da karin gudummawa kan harkokin da suka shafi kasashen Afirka.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Gabon a harkokin gudanarwar taron kolin FOCAC, a sa'i daya kuma, tana son yin kokari ta hanyar gudanar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", ta yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka bisa manyan tsare tsare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China