in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNOCHA: An aikata ayyukan cin zarafin ma'aikatan jin guda 78 a Sudan ta kudu a watan Agusta
2018-09-19 13:17:56 cri

Hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD ta ba da rahoton aikata ayyuka kusan 78 da suka shafi cin zarafin ayyukan ba da agaji a watan Agustan wannan shekara a kasar Sudan ta kudu, galibi ayyukan sun fi faruwa ne a jihohin Jonglei da tsakiyar Equatoria da kuma Upper Nile.

Ofishin na UNOCHA ya ce, daga cikin wannan adadi, kaso 23 cikin 100 ya shafi cin zarafin ma'aikatan jin kai ne, sai kuma kaso 26 cikin 100 da ya shafi barnata kayayyakin jin kai.

Hukumar wadda ta bayyana hakan cikin wani sabon rahoto da ta fitar, ta ce, wannan ya nuna yadda ma'aikatan hukumar ke fuskantar kalubale wajen shiga muhimman wuraren da mutane ke bukatar agaji, inda ake barin fararen hula da ma'aikatan agaji da ma kayayyakin agaji ba tare da matakan tsaro ba.

Shekaru biyar ke nan da kasar Sudan ta kudu ta fada tashin hankalin da yake mummunan tasiri kan al'ummar kasar, lamarain da ya haifar da daya daga karuwar matsalar 'yan gudun hijira mafi girma a duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China