in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhawarar kwamitin sulhu na MDD na watan Nuwamba zai mayar da hankali kan huldar kasa da kasa da wanzar da zaman lafiya a Afrika
2018-11-02 11:34:38 cri
Yayin da kasar Sin ke rike da ragamar shugabancin karba-karba na kwamitin sulhu na MDD a wannan karon, Jakadan kasar a MDD Ma Zhaoxu ya ce, muhawarar kwamitin a watan nan na Nuwamba, za ta mayar da hankali kan huldar kasa da kasa da wanzar da zaman lafiya a Afrika.

Ma Zhoaxu ya ce, ana fuskantar kalubale masu tsanani game da yanayin tsaron kasa da kasa. A lokaci guda kuma ana yi wa dokoki da huldar kasa da kasa tarnaki.

Ya shaidawa manema labarai cewa, dole ne kwamitin wanda ke da hakkin wanzar da tsaro da zaman lafiya a duniya, ya jagoranci karfafa huldar kasa da kasa da samar da dabarun tsaro na bai daya.

Ya ce huldar kasa da kasa babban maudu'i ne da aka yi tafka muhawarar kansa yayin zaman babban zauren majalisar a watan Satumba, inda kasashe fiye da 100 suka bayyana ra'ayinsu na mara mata baya.

Dangane da wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afrika kuwa, Jakadan na Kasar Sin ya bayyana fatan muhawar da za a yi ranar 20 ga wata, za ta taimaka wajen samar da dandalin kara tattauna batun. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China