in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin samar da abinci da raya aikin gona na MDD sun nuna goyon baya ga manufofin Sin na farfado da kauyuka
2018-11-03 17:06:54 cri
Hukumomin samar da abinci da raya aikin gona na MDD, wadanda suka hada da FAO da IFAD da WFP, sun bayyana amincewarsu ga manufofin kasar Sin na farfado da kauyuka, inda suka ce, manufofin sun dace da burikansu a wannan fanni.

Hukumomin tare da hadin gwiwar ma'aikatar kula da aikin gona da kauyuka ta kasar Sin, sun bayyana haka ne cikin wata hadaddiyar sanarwa da suka fitar jiya a birnin Changsha na kasar Sin, yayin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasashe masu tasowa a fannin aikin gona a duniya.

Wannan shi ne karo na farko da MDD ta nuna goyon baya ga manufofin farfado da kauyuka na kasar Sin ta hanyar gabatar da takarda a hukunce. Cikin sanarwar, hukumomin uku, sun yabawa kasar Sin bisa tsayuwar daka da ta yi kan raya aikin gona da kauyuka, ciki har da zuba jari ga ginin ababen more rayuwa, da makamashi, da fasahohin zamani ba tare da gurbata yanayi ba, suna masu cewa, ta haka za a yi yaki da talauci da tabbatar da wadatuwar abinci mai dorewa.

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana son cin gajiyar fasahohinta da hukumomin uku na MDD yayin da take aiwatar da manufofin farfado da kauyuka, don samar da gudummawa ga kasashe masu tasowa wajen cimma ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China