in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya murnar taro kan intanet na kasa da kasa karo na biyar
2018-11-07 13:44:08 cri
A yau Laraba, aka kaddamar da taro kan intanet na kasa da kasa karo na biyar a garin Wuzheng dake lardin Zhejiang. Sabo da haka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tura sakon taya murnar kaddamar da taron.

A cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, a halin da ake ciki a duniya, ana fuskantar wani babban sauyin kimiyya da fasaha da yake shafar fannoni masu dimbin yawa. Ana kuma samun babban ci gaba a fannonin fasahohin zamanin yanzu, kamar su intanet da amfani da bayanai masu tarin yawa da kuma na'urorin mutumi-mutumin da suke da basirar dan Adam, wato AI a takaice. Sakamakon haka, kasashe daban daban suke dogaro da juna domin cin moriya. Sabbin fasahohin zamani sun kuma samar da sabon karfi ga aikin bunkasa tattalin arziki. Yanzu ana bukatar hanzarta bunkasar tattalin arziki bisa ilmin dake da nasaba da bayanai, sannan a ciyar da ayyukan tafiyar da shafukan intanet gaba cikin adalci da gaskiya.

Shugaba Xi ya kuma nanata cewa, ko da yake halin da kowace kasa take ciki ya sha bamban sosai, kuma suna kan matakai daban daban wajen bunkasa intanet, kana suke fuskantar kalubale daban daban, amma suna da buri daya na bunkasa tattalin arziki bisa ilmin bayanai, da kuma shawo kan kalubalen da suke fuskanta a shafukan intanet. Ya ce ya kamata kasa da kasa su karfafa hadin gwiwarsu ta a zo a gani bisa ka'idar neman ci gaba tare domin kokarin cimma nasara tare. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China