in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan gidan talabijin na SVT na kasar Sweden saboda cin zarafin kasar Sin
2018-09-25 09:50:18 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a jiya Litinin cewa ta yi Allah wadai da babbar murya kuma ta bayyana bacin ranta ga gidan talabijin din kasar Sweden SVT, sakamakon cin zarafin da ya yiwa kasar Sin a cikin wani shirin labarai da ya gabatar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Geng Shuang shi ne ya yi wannan tsokaci a lokacin da aka bukaci ya yi karin haske game da shirin wanda gidan talabijin na kasar Sweden ya watsa mai kunshe da cin mutunci da cin fuska ga kasar Sin, wanda ya watsa da yammacin ranar Juma'a.

Shirin na SVT ya ci mutuncin kasar Sin kana ya yi wa Sinawa kazafi, in ji Geng, ya kara da cewa, mai sanya ido kan jagorancin shirin talabijin din cike yake da halayyar nuna banbanci, da nuna son kai, da kuma nuna tsokana ga kasar Sin da sauran kabilu, wanda hakan ya kaucewa ka'idojin gudanar da aikin yada labarai.

A cewar kakakin, kasar Sin ta bukaci mutanen dake da ruwa da tsaki a game da shirin da su gaggauta daukar matakan da suka dace wajen kawar da masu neman zubarwa kasar Sin kimarta kana kasar Sin tana da ikon da za ta iya daukar matakan da suka dace. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China