in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ce ta nuna bukatar dage tattaunawa da Sin game da diflomasiya da tsaro, in ji Hau Chunying
2018-10-04 15:15:25 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta jaddada cewa, kasar Amurka ce ta gabatar da bukatar dage zaman tattaunawa, tsakanin wakilanta da na kasar Sin, game da batutuwan da suka jibanci harkokin diflomasiyya da tsaron kasashen biyu, sabanin yadda wasu kafofin watsa labaru ke bayyana akasin hakan.

Hua Chunying ta ce, wasu kafofin watsa labarun Amurka, sun rika yada jita jitar cewa, wai Sin ce ta nemi a dage tattaunawar, wanda hakan ya sabawa gaskiyar halin da ake ciki. Ta ce yada wadannan kalamai, na nufin kafofin na da wata boyayyiyar manufa da suke son su cimma, kana hakan ya sabawa hali na gari.

Jami'ar ta kara da cewa, Sin na Allah wadai da wannan zargi, tana kuma fatan sassan dake yada wannan jita jita za su dakatar da aikata hakan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China