in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana matukar adawa da shigar jirgin ruwan yaki na Amurka sassan tekun kudancin kasar
2018-10-02 15:14:57 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin uwargida Hua Chunying, ta ce kasar Sin na matukar Allah wadai da shigar jirgin ruwan yaki na Amurka, yankunan tsibiranta dake tekun kudancin kasar.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne a Talatar nan, tana mai cewa a ranar 30 ga watan Satumba, ba tare da neman izini daga gwamnatin Sin ba, wani jirgin ruwa na yaki mallakar Amurka, ya ratsa yankunan tsibiran Nansha na kasar Sin. Sai dai nan take rundunar sojin ruwan kasar Sin ta gano jirgin, inda ta gargadi matukan sa, ta kuma kore shi daga yankin.

Jami'ar ta ce ko shakka babu, tsibiran Ninsha mallakin kasar Sin ne. kuma hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashe mambobin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, na kara kyautata yanayin da ake ciki a yankin. To sai dai kuma matakan tsokana da Amurka ke aiwatarwa, na yin kutse da sunan 'yancin zirga zirga a teku, na barazana ga zaman lafiya da daidaito da ake da shi a yankin.

Hua Chunying ta kara da cewa, irin wadannan matakai da Amurka ke dauka, sun saba burin kasashen yankin, da ma halaye da kasashen duniya suka amince da su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China