in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sergei Lavlov ya yi magana da Mike Pompeo
2018-07-22 16:18:22 cri
Shafin yanar gizo na Intanet na ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya bada labari a jiya 21 ga wata cewa, ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavlov ya bugawa takwaransa na kasar Amurka Mike Pompeo wayar tarho, don tattaunawa kan dangantakar dake tsakanin kasashensu.

An ce, bayan shugabannin kasashen biyu sun gana da juna a ranar 16 ga wata, sai ministocin harkokin wajen biyu suka bugawa juna waya a wannan rana don yin musanyar ra'ayi kan makomar bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu bisa tushen daidaituwa da kawo moriyar juna da dai sauran batutuwa. Hakazalika, sun tattauna kan wasu manyan batutuwa ciki hadda halin da Sham da wuraren dake dab da ita suke ciki, da batun jin kai ga kasar Sham dake da nasaba da sauran kasashe da dai sauransu, tare kuma da yin musayar ra'ayi kan sa kaimi ga kawar da makaman nukiliya a zirin Korea.

Shugaban Amurka Trump da takwaransa na Rasha Valadimir Putin sun gana da juna a ranar 16 ga wata a birnin Helsinki na kasar Finland. Fadar shugaban Amurka ta sanar a ranar 19 ga wata cewa, Trump ya nemi mai taimaka masa kan harkokin tsaron kasar John Bolton da ya gayyaci Putin don ya kai ziyara a kasar a lokacin kakar bana. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China