in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Amurka da Rasha: Ganawarsu na da ma'ana
2018-07-17 13:30:05 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar Rasha Valadimir Putin sun tattauna a birnin Helsinki, hedkwatar kasar Finland, inda suka bayyana ganawar tasu karon farko a matsayin mai ma'ana, tare da cewa za su ci gaba da tutunbar juna nan gaba.

Shugabannin biyu sun yi ganawar sirri da ta shafe sa'o'i da dama a fadar shugaban Finland. Yayin taron manema labaru da aka yi bayan ganawartasu, Shugaba Trump ya ce, sun tattauna kan wasu manyan batutuwa dake jan hankalinsu ciki hadda batun zargin da aka yi wa Rasha na sa hannu cikin babban zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016, da batun makaman nukiliyar zirin Koriya, da yaki da ta'adanci, da kuma halin da Iran da Sham ke ciki.

Trump ya ce, shawarwarin nasu na da ma'ana, kuma kwamitocin kasashen biyu za su kara tattaunawa kan wadancan abubuwa a nan gaba, inda ya ce ganawar ta zama sharar fage ga tattaunawarsu a nan gaba.

A nasa bangare kuma, shugaba Putin ya ce, ya gamsu sosai da ganawar ta wannan karon, ko da yake ba za ta iya warware dukkanin matsaloli dake tsakaninsu ba, amma ta zama hanyar da ta dace da za su bi. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China