in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Moscow za ta mayar da martani yadda ya kamata kan takunkumin da Amurka ta kakaba mata
2018-08-24 10:13:16 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyabna cewa, kasarta za ta mayar da martani ta hanyar da ta dace kan sabbin takunkuman da kasar Amurka ta kakaba mata.

Zakharova wadda ta bayyana hakan jiya Alhamis yayin taron manema labarai ta ce, sanin kowa ne cewa, Rasha za ta mayar da martanin da ya dace kan takunkumin da Amurka ta sanya mata walau sabo, ko wanda ta sabunta ko ta yiwa gyaran fuska. Haka kuma Rashar ba za ta sanar da hanyoyin da za ta dauka kan wannan mataki ba.

Ta kara da cewa, Rasha ta sha nanatawa cewa, ba za ta kasance wadda za a fara sanyawa wata kasa takunkumi ba, amma kuma za ta dauki matakan da suka dace don mayar da martani kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata.

A farkon wannan watan ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa, za ta kakabawa kasar Rasha sabbin takunkumai da za a kasa su gida biyu. Mataki na farko na takunkumin ya fara aiki ne a ranar 22 ga watan Agustan da muke ciki.

Kasashen Rasha da Amurka sun saba sanyawa juna takunkumi, yayin da dangantaka a tsakaninsu ke ciki da yin tsami a 'yan shekarun nan. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China