Zakharova wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, ta ce kusoshin siyasa a Amurka sun kasa gane cewa, takunkumi ba zai iya tilasawa Rasha barin hanyar da ta zaba domin kare manufofin ci gaban kasa ba.
Amurka dai ta fara aiwatar da sabon takunkumin da ta kakabawa Rasha ne tun daga ranar Litinin, bisa zargin ta da hannu wajen sanyawa tsohon dan leken asirin kasar Sergei Skripal da 'yar sa Yulia guba, a wani wurin cin abinci dake garin Salisbury na kasar Birtaniya, tun cikin watan Maris da ya shude. To sai dai kuma Moscow ta dade tana musanta wannan zargi.
Takunkumin na Amurka dai ya shafi hana Rasha damar samun wasu kayayyakin sarrafawa, da na fasahohin zamani masu nasaba da tsaron Amurka. Sauran sun hada da hana kasar sayen wasu kayayyaki na laturoni, da na kere kere da suka jibanci fannin mai da iskar gas. (Saminu)