Ma'aikatar ta ce, wadanda aka sanya musu takunkumin sun hada da kungiyoyi biyu da daidaikun jama'a biyu dake da alaka da kasar Rasha. Bisa dokokin da suka shafi muggan ayyukan yanar gizo na Amurka, ma'akatar ta yi zargin cewa, sun kaucewa takunkumin kasar, ta hanyar taimakawa wata kungiyar kasar Rasha, wadda ta sanyawa takunkumi. A wannan gaba kuma, Amurka ta kuma sanya takunkumi kan wasu kungiyoyi biyu da jiragen ruwa 6 dake da alaka da Rasha, sakamakon zarginsu da ake na mika tataccen mai tsakaninsu da wasu jiragen ruwa masu rataye da tutar kasar Koriya ta arewa. (Bilkisu)