in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin raya Afrika yana goyon bayan zuba jari don cigaban nahiyar ta Afrika
2018-11-08 10:11:11 cri
Cibiyoyin samar da kudade suna goyon bayan Afrika a yunkurin da take na janyo hankalin masu zuba jari da kuma yadda take kokarin cike gibin kayayyakin more rayuwar jama'a a nahiyar, Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya ci gaban Afrika (AfDB) shi ne ya bayyana hakan.

Da yake jawabi a lokacin taron dandalin Afrika game da zuba jari a Johannesburg, shugaban bankin na AfDB ya ce, duk da irin dimbin kalubalolin da ake fuskanta a nahiyar, amma duk da haka nahiyar Afrika tana da abubuwa masu tarin yawa da za ta gabatarwa masu sha'awar zuba jari. "Afrika tana da albarkatu masu dimbin yawa, ma'adanai, mai da aikin gona. Muna son mu fito da abubuwan da Afrika ke da su. Mu a matsayinmu na cibiyar gudanar da harkokin kudi muna goyon bayan Afrika a matsayin wani muhimmin wajen zuba jari," in ji shi.

Biyar daga cikin 10 na wuraren da aka fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya yana nan a Afrika, in ji Adesina.

"Zuba jari a Afrika. Za mu iya zama wata babbar kasuwa. Muna son za mu samar da muhimman kayayyakin more rayuwa. Muna son ci gaban Afrika cikin sauri," in ji shi.

Adesina ya bayyana cewa sauye sauye da suka hada da dokokin gudanar da ayyuka, da sauya fasalin tsare tsare wajen aiwatar da ayyuka masu yawa a kasashen Afrika a shekaru masu yawa da suka gabata za su samar da kyakkyawan muhallin yin cinkayya a nahiyar Afrika.

Adesina ya yi amanna cewa, taron dandalin zuba jarin da ake gudanarwa za'a yi amfani da shi wajen tsara dabarun zuba jari na dogon lokaci wanda zai taimakawa bunkasuwar Afrika.

Ana sa ran za'a sanar da kulla yarjejeniyoyi na ayyukan biliyoyin dalolli a lokacin dandalin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China