in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi hasashen tattalin arzikin Ghana zai bunkasa cikin sauri a 2018
2018-03-15 09:43:08 cri

Hasashen da hukumomin kasa da kasa suka yi wanda ya nuna cewa Ghana za ta samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri a cikin wannan shekara ya yi daidai da hasashen da ita kanta gwamnatin Ghanan ta yi, Edward Asuo-Afram, shugaban sashen kididdigar tattalin arziki na kasar (GSS), ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a jiya Laraba.

Jaridar The New York Times ta wallafa hasashen da bankin duniya, asusun ba da lamuni na IMF, da bankin raya ci gaban kasashen Afrika (AfDB) suka yi, na cewa da alama, Ghana za ta sha gaban Indiya wajen samun karuwar tattalin arziki, kuma za ta kasance kasar da tattalin arzikinta zai fi na kowace kasa bunkasuwa cikin sauri a fadin duniya a shekarar 2018.

Masu nazari kan al'amurra sun danganta yiwuwar samun karfin tattalin arzikin kasar ta Ghana sakamakon karuwar farashin kayayyaki, da bunkasar samar da albarkatun mai, da kuma matsayin da kasar ta samu na zama kasa ta biyu a duniya dake samar da koko don cefanar da shi a kasuwannin duniya.

Rahoton ya kara da cewa, kasar ta yammacin Afrika tana kara fita daga cikin yanayin kangin talauci wanda ya jima yana addabar ta a bisa tarihi.

Rahoton jaridar na The New York Times ya kara da cewa: "Hasashen da aka yi a halin yanzu ya nuna cewa, tattalin arzikin Ghana zai karu daga kaso 8.3 zuwa kaso 8.9 bisa 100 a shekarar ta 2018."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China