in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Wasu kasashen Afirka sun karfafa yin kirkire-kirkire don bunkasa tattalin arzikinsu
2018-07-11 09:28:59 cri
Wani rahoto game da harkokin kirkire-kirkiren kasa da kasa na shekarar 2018 da aka kaddamar a biranen Nairobi da New York ya nuna cewa, kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara suna karfafa harkokin kirkire-kirkire a wani mataki na bunkasa tattalin arziki da makomar kasashensu.

Wadannan kasashe a cewar rahoton mai take, "Zaburar da duniya da harkokin kirkire-kirkire" sun hada da Afirka ta kudu da Kenya da Mauritius da kuma Rwanda. Inda ya nuna cewa, cin gajiyar kimiya da fasahar kere-kere, da ilimi mai zurfi da kwararrun ma'aikata sun karfafawa tattalin arzikin kasashen na Afirka gwiwar yin takara.

Alkaluman rahoton sun nuna cewa, tun daga shekarar 2012 kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara ne, suke cikin kungiyoyin da suka yi nasara a wannan fanni.

A halin da ake ciki kuma wani rahoto da kugiyar kare 'yan cin mallakar fasaha ta duniya (WIPO) da abokan hulda daga jami'o'I da sauran masu ruwa da tsaki a wannan harka suka wallafa, sun nuna cewa, yana da muhimmanci kasashen na Afirka su rike matsayin da suke a wannan fanni .(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China