in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin kasar Uganda yayi hasashen karuwar tattalin arzikin kasar da kaso 6.5 bisa dari cikin shekaru 3 masu zuwa
2018-04-09 21:15:27 cri
Babban bankin kasar Uganda yayi hasashen karuwar tattalin arzikin kasar da kaso 6.5 bisa dari cikin shekaru 3 masu zuwa. Gwamnan babban bankin kasar Tumusiime Mutebile, ya bayyanawa manema labarai a Litinin din nan cewa, nasarar hakan na da nasaba da yanayin da sauran kasashe ke ciki a fannin raya tatttalin arziki, da kuma damammaki da kasar ke da su sakamakon makudan kudaden jari da sassan gwanmati da na masu zaman kansu suke zubawa.

A cewar Mutebile, wasu alkaluma da hukumar kididdigar kasar ta fitar sun nuna irin ci gaban da tattalin arzikin kasar Uganda ya samu a shekarar 2017 wanda ya kai kaso 6.3 bisa dari, sama da kaso 3 bisa dari da kasar ta samu a shekarar 2016.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China