in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin Najeriya zai cigaba da kiyaye manufofin kudi na kasar
2018-09-26 11:04:32 cri

Babban bankin Najeriya zai cigaba da kiyaye tsarinsa game da manufar kudin kasar wato (MPR) a takaice na kashi 14 bisa 100 a karo na 13 a jere.

Wannan na nufin kudaden ajiya na wajibi ga bankuna za su ci gaba da kasancewa kaso 22.5 bisa dari, yayin da na jarin ajiya domin biyan basussukan bankuna zai kasance kaso 30 bisa dari, Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar.

Emefiele ya ce kwamitin kula da harkokin kudi na kasar (MPC) ya yi la'akari da tasirin da kudaden ajiyar zai iya yi sakamakon kashe makudan kudade a kasar dake da nasaba da babban zaben kasar, da kuma karuwar kudaden da ake baiwa jahohin kasar daga cinikin danyane man fetur na kasar.

Ya kara da cewa, dole ne kwamitin ya takaita yawan kudaden da ake kashewa domin gudun kada a kara fadawa cikin matsalar tashin farashin kayayyaki wanda a halin yanzu ya karu daga kashi 11.14 a watan Yuli zuwa kashi 11.23 a watan Agusta.

Emefiele ya ce, kwamitin kudin kasar ya nuna damuwa sakamakon yawaitar kudaden basusukan da ake bayarwa wadanda basa amfani a tsarin bankunan kasar da kuma yawan karuwar kalubaloli da matsin lamba ga tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China