Ministan kudi da raya tattalin arziki na kasar Bostswana Kenneth Matambo Minista shi ne ya bayyana hakan yayin bude taron majalisar ministocin kungiyar SACU karo na 35 da ya gudana jiya a Gaborone, fadar mulkin kasar Botswana. Ya ce kasashen dake kungiyar sun yi hasashen samun matsakaicin ci gaba, ganin tarin damammakin da suka karade duniya wadanda ci gaban tattalin arziki duniya ya kawo.
Ya ce, yayin da kasashe mambobin SACU ke da tabbaci game da makomar ci gaban duniya, suna kuma nuna damuwa game da yadda ake ba da kariya ga harkokin cinikayya da karuwar cacar-bakin cinikayya tsakanin Amurka a hannu guda da kuma abokan cinikayyarta a daya bangaren.
A don haka Matambo ya ce, akwai bukatar tattaunawa tsakanin kasashe, don cimma daidaito ta yadda za a warware wadanan matsaloli.(Ibrahim)