in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaurara tsaro a babban birnin Nijeriya bayan rikicin da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da masu zanga-zanga
2018-11-02 10:49:42 cri
An tsaurara matakan tsaro a Abuja babban birnin Nijeriya, biyo bayan rikicin da ya barke baya-bayan nan tsakanin dakarun gwamnati da daruruwan masu zanga-zanga.

An ga jami'an tsaro a jiya, dauke da manyan makamai a manyan titunan tsakiyar birnin, da kuma hanyoyin shiga da fita daga birnin, ciki har da hanyar da ta dangana da majalisun dokokin kasar da kuma sakatariyar gwamnati.

Haka zalika, motocin 'yan sanda masu jiniya sun yi ta sintiri a wasu sassan birnin domin tabbatar da harkokin da zirga-zirgar mutane da kayayyaki sun koma yadda suke.

zanga-zangar neman sakin wani shugaban addini ne ya rikide zuwa rikici a Abuja, lokacin da masu zanga-zangar suka yi arangama da dakarun tsaro. Hatsaniyar ta tsai da harkoki a wajen birnin na Abuja tsawon sa'o'i.

Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da an harbi masu zanga-zanga 3 har lahira, sai dai wasu majiyoyi sun ce mutane 6 ne suka mutu sannan wasu da dama sun raunana.

Mabiya mazhabar shi'a ne suka gudanar da zanga-zangar domin neman sakin shugabansu Ibrahim El-Zakzaky, wanda jami'an tsaron farin kaya suka tsare tun watan Disamban 2015, bayan wani rikici da ya barke tsakanin mabiyansa da dakarun tsaro a jihar Kaduna dake arewacin kasar.

Da yake mayar da martani game da rikicin a ranar Larabar da ta gabata, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan kula da birnin tarayya da ya ja ragamar kula da lamarin ta hanyar kafa wani kwamitin tsaro.

A nasa bangaren, babban sufeton 'yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris, ya ce kawo yanzu, masu zanga-zanga 400 aka tsare. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China