Shugaban hukumar INEC Mahmood Yakubu, ya ce jimilar mutane 6,352 ne za su tsaya takarar mambobin majalisun dokokin kasar biyu. Sannan jam'iyyun siyasa 91 za su fafata a babban zaben na 2019.
Mahmood Yakubu ya bayyanawa manema labarai a jiya cewa, ana ci gaba da shiryawa zaben yadda ya kamata, bisa tanadin jadawalin zaben da hukumar ta riga ta fitar. (Fa'iza Mustapha)