in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da wakilan shugabannin kamfanonin waje masu halartar bikin CIIE
2018-11-05 13:33:03 cri

A yau Litinin 5 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan shugabannin kamfanonin waje, masu halartar bikin baje koli na CIIE a birnin Shanghai.

Yayin ganawar ta su, Shugaba Xi ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40, tun bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, Sin tana kara kyautata cudanya, da hadin kanta da kasashen duniya. Kaza lika Sin na yin kokari tare da kasa da kasa wajen raya makomar bil Adama ta bai daya.

Xi ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta dakatar da takenta na bude kofa ga waje, da yin gyare-gyare a gida ba, maimakon hakan za ta kara bude kofarta ga ketare. Yanzu Sin ta riga ta fitar da jerin matakan bude kofarta, kuma shirya bikin CIIE, daya ne daga cikinsu. Game da matsalolin da za a samu yayin da Sin ke inganta hadin gwiwa tare da ketare, Sin za ta nemi duk hanyar da ta dace wajen warware su. Kana kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan muhalli ga kamfanonin ketare, wajen zuba jari domin cimma moriya da nasara tare.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China