Yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ganawa da firayin ministan kasar Rasha Dmitri Medvedev a birnin Shanghai.
Yayin ganawarsu, Xi ya yi nuni da cewa, matsaya guda da suka cimma tare da shugaban Rasha Vladimir Putin kan hadin gwiwiar dake tsakanin Sin da Rasha, abu ne mai matukar muhimmanci ga kasashen biyu, ya kamata sassan biyu su kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin makamashi da aikin gona da harkar kudi da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sauransu.
Xi ya kara da cewa, yana maraba da kasar Rasha da ta halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa kasar daga ketare karo na farko da ake gudanarwa a birnin Shanghai, yana fatan Rasha za ta nuna wa duniya kayayyaki masu halayyar musamman ta Rasha.
A nasa bangare, Medvedev ya bayyana cewa, ya godewa kasar Sin bisa ga gayyatar Rasha bikin baje kolin a matsayin babbar bakuwa, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, kuma daga yanzu Rasha za ta ci gaba da halartar bikin ko wace shekara, kana Rasha tana son hada kai tare da kasar Sin domin tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za su kara habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, haka kuma za su kara yin cudanya da musanyar ra'ayoyi kan harkokin kasa da kasa, tare kuma da kiyaye ka'idojin kasa da kasa da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya yadda ya kamata.(Jamila)