in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#CIIE# Xi Jinping ya halarci farkon baje kolin CIIE, kuma ya gabatar da wani jawabi
2018-11-05 10:12:47 cri
Da safiyar yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci farkon baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE, inda ya kuma gabatar da wani muhimmin jawabi. A cikin jawabin shugaba Xi ya wakilci gwamnati da al'ummar kasar Sin, wajen yin maraba da baki wadanda suka fito daga kasashe, da yankuna, da kungiyoyin kasa da kasa 172, da kamfanoni da masana'antu fiye da 3000, da su halarci wannan biki da hannu bibbiyu. Ya kuma yi fatan abokai wadanda suka fito daga kasashe daban daban, za su yi amfani da wannan dama da aka samu, sakamakon bunkasar kasar Sin, domin zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a iya samun bunkasa da ci gaba tare. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China