Xi Jinping ya kara da cewa, ya kamata a fili kasashe daban daban su nuna adawa da manufofin kafa shinge ga cinikayyar da ake yi tsakanin kasa da kasa, da daukar matakai na kashin kai, ya kamata su yi kokarin bin manufar daidaita harkoki tsakanin bangarori daban daban, da daga matsayin bude kofofinsu, ta yadda za a iya ingiza yin mu'amalar tattalin arziki tsakaninsu, da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa.
Bugu da kari, ya kamata kasashe daban daban su kara daidaita manufofi, da matakansu na bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa daga dukkan fannoni, domin rage matsalolin dake kawo musu illa. A waje daya, Xi Jinping yana fatan a kafa wani sabon tsarin tattalin arziki da cinikayya cikin adalci, da gaskiya, ba tare da boye komai ba, ta yadda za a iya saukaka sharudan yin cinikayya, da zuba jari da a kara bude kofa, da yin mu'amala, da hadin gwiwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa. (Sanusi Chen)