in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta amince da dokar da za ta dakile samuwar kudade ga kungiyoyin 'yan ta'adda
2018-10-10 09:30:33 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta bayyana goyon baya ga majalissar dokokin kasar, bisa amincewa da dokar CFT, wadda ta tanaji datse hanyoyin da 'yan ta'adda ke bi su tara kudade, dokar da ta yi daidai da kudurin MDD mai nasaba da hakan.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya Talata ta nuna cewa, matakin tabbatar da wannan doki, zai dakatar da aniyar kasar Amurka, na kakabawa Iran din takunkumi.

A ranar Lahadin karshen mako ne dai 'yan majalissar kasar ta Iran, suka amince da tanajin dokar ta CFT, wadda ta yi daidai da tanaje tanajen da hukumar FATF ta yi, game da yaki da safarar haramtattun kudade, ko barazanar tattara kudade tsakanin kunyiyoyin 'yan ta'adda, da kuma duk wata barazana ga cibiyoyin hada hadar kudade na kasa da kasa.

An dai kafa hukumar FATF ne a shekarar 1989, tana kuma hadin gwiwa da kasashe da yankuna daban daban, wajen yaki da yaduwar haramtattun kudade, da wadanda ke iya shiga hannayen kungiyoyin ta'addanci.

Kasashen Amurka da Isra'ila, da Saudi Arabia da kawayen su, sun sha yunkurin ganin an sanya kasar Iran, cikin jerin kasashen da FATF za ta yiwa bakar lamba. To sai dai kuma kungiyar ta sanya watan nan na Oktoba, a matsayin wa'adi na karshe ga Iran, da ta kammala sauye sauye da suka wajaba, wadanda za su yi daidai da tsarin sauran kasashen duniya a wannan fanni, ko ta fuskanci hukunci. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China