in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya koma gida daga Amurka bayan ya tsallake rijiya daga hadarin jirgin sama
2018-10-01 16:04:02 cri
Kafafen yada labarai na cikin gidan kasar Ghana sun bada rahoton komawar shugaban kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo gida a jiya Lahadi bayan ya tsallake rijiya da baya a lokacin da jirgin shugaban kasar ya kusa yin hadari a birnin Washington D.C. na Amurka da yammacin ranar Asabar.

Ministan yada labaran kasar mai jiran gado, Kojo Oppong Nkrumah, wanda ya yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan isar shugaban kasar gida, ya tabbatar da cewa, daya daga cikin injunan jirgin saman shugaban kasar wanda ke dauke da shugaban da sauran 'yan tawagarsa wadanda suka halarci babban taron MDD ya fuskanci tangarda mintoci 20 bayan ya tashi sama a birnin Washington D.C.

Majiyar ta shedawa kafafen yada labarai cewa jirgin saman samfurin Falcon 900 ya tashi ne a babban birnin kasar Amurka inda ya kone man dake cikinsa, kafin daga bisani aka taimakawa jirgin ya sauka kasa.

Nkrumah ya ce, daga bisani Akufo-Addo da sauran 'yan tawagar tasa sun koma kasar ta Ghana ne a wani jirgin 'yan kasuwa na kasar Afrika ta kudu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China