An samu karuwar adadin ne bayan jami'ai a jihar sun tabbatar da mutuwar karin mutane 23 da jikkatar wasu 17, sakamakon bazuwar da rikicin ya yi zuwa birnin jihar a ranar Lahadin da ta gabata.
Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Ben Kure, ya ce gwamnati na kokarin shawo kan rikicin.
Rikicin na baya-bayan nan a Kaduna, wadda ta kasance daya daga cikin jihohin da ta fuskanci yawan hare-hare a kasar, ya fara ne a ranar Alhamis da ta gabata a Kasuwar Magani, wani kauye dake da nisan kilomita 31 daga birnin jihar.
Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne sanadiyyar sabanin da aka samu kan wurin da 'yan kasuwa za su rika sauke kayansu na sayarwa a ranar Alhamis da ake cin kasuwar kauyen. Da farko, mutane 50 ne aka tabbatar sun mutu. (Fa'iza Mustapha)