Mr. Ma Zhaoxu ya fadi haka ne a yayin da yake jawabi a lokacin bikin kaddamar da rahoton nazarin ayyukan gona da bangaren Sin zai samarwa kasashen Afirka da hukumar hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin da hukumar tsara shirin neman ci gaba ta MDD suka shirya tare.
Sannan Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kaddamar da wannan rahoto na nazarin ayyukan gona da bangaren Sin zai samarwa kasashen Afirka wani mataki ne da aka dauka domin aiwatar da shirye-shiryen da aka fitar a taron kolin FOCAC da aka yi a watan Satumban bana.
Ma Zhaoxu ya kara da cewa, an riga an shiga shekara ta 3 da fara aiwatar da shirin neman dawwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 na MDD. Nahiyar Afirka nahiya ce dake da kasashe maso tasowa mafi yawa, tana fuskantar kalubaloli masu tsanani wajen aiwatar da shirin. Ya kamata gamayyar kasa da kasa su hanzarta taimakawa kasashen Afirka wajen kawar da talauci da yunwa da rashin kayayyakin more rayuwa da suka fi jawo hankulan al'ummomin kasashen Afirka, sannan a hanzarta bunkasa masana'antu a kasashen Afirka ba tare da tangarda ba. (Sanusi Chen)