in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban 'yan aware a Nijeriya ya yi watsi da kiran da abokin hammayarsa ya yi na a kauracewa babban zaben 2019
2018-10-23 10:16:15 cri
Shugaban kungiyar 'yan aware dake rajin balle yankin kudu maso gabashin Nijeria mai arzikin mai fetur cikin kwanciyar hankali, wato Ralph Uwazurike, ya yi kira ga magoya bayansa, da su yi watsi da kiran da kungiyar hammayarsu ta yi wa al'ummar yankin na kauracewa babban zaben kasar na 2019.

Ralph Uwazurike, wanda shi ne shugaban kungiyar dake kokarin tabbatar da kasar Biafra wato MASSOB, ya yi gargadin ne jiya a birnin Owerri dake kudancin kasar.

Shi kuma shugaban kungiyar 'yan asalin Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu, wanda ya bayyana a kasar Isra'ila, ya sanar cikin wani sakon bidiyo da ya fitar cewa, babu wani zabe da zai gudana da a yankin kudu maso gabashin kasar a 2019.

Ralph Uwazurike ya ce irin wannan kiran abun dariya ne, saboda Nnamdi Kanu ba shi ke da ikon gudanar da zabe a Nijeriya ba, kuma niyyarsa ita ce, ingiza mambobin kungiyar su tada rikicin da zai haifar da asarar rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Cikin sakon bidiyon, Nmadi Kanu ya ce nan ba da dadewa ba zai koma Nijeriya ya farfado da fafutukar neman 'yancin Biafra.

Rabon da a ji duriyar Nnamdi Kanu tun cikin watan Yuli da rundunar sojin kasar ta kaddamar da aikin kawo karshen harkokin kungiyar IPOB.

Ralph Uwazurike, ya ce an horar da Nnamdi Kanu ne don ya kawo cikas ga ayyukan kungiyar MASSOB, yana mai cewa dalilin da ya sake bayyana shi ne, ya yi amfani da kungiyar IPOB da nufin samun kudi domin bukatun shi na kashin kai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China