in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a rika tabbatar da furuci a aikace game da karfafawa mata domin samun zaman lafiya
2018-10-26 10:19:34 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya da su rika tabbatar da furucinsu a aikace, game da karfafawa mata a fannin samar da zaman lafiya da tsaro.

Antonio Guterres ya shaidawa taron muhawarar manyan jami'an Kwamitin Sulhu na MDD kan mata da zaman lafiya da tsaro cewa, akwai babban gibi tsakanin furucin da ake yi da abun da ake aiwatarwa game da batun.

Ya ce a kowace shekara, a kan dauki nagartattun kudurori, amma kuma ba a samar musu da kudade da kudurorin shugabanci da ake bukata. Haka zalika, a kan maimaita kididdiga game da dorewar tsarin zaman lafiya da ya kunshi kowa, amma kuma ba a hakan ake sulhunta yawancin rikice-rikice ba.

Har ila yau, ya ce a kan bayyana kyawawan tasirin ga harkar samar da zaman lafiya, amma kuma dama kalilan ake ba su. Kana a kan dogara sosai da kungiyoyin mata, sai dai ba a samar musu da isassun kudade. Sannan kuma ana sane da muhimmancin daidaiton jinsi, amma kuma sai a rage kason kudaden tabbatar da shi.

Antonio Guuterres, ya yi alkawarin daukar jerin matakan cike gibin a shekara mai zuwa, ciki har da samun mata masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da inganta rawar da mata ke takawa wajen shiga tsakani da kuma samar da karin kudaden tabbatar da daidaiton jinsi don samar da tsaro da zaman lafiya.

Ya ce daidaiton jinsi na da gagarumar damar yin kyakkyawan tasiri kan ayyuka da nagartar harkokin MDD. Sai dai a wannan fannin ake samun adadi da sauyi mafi karanci. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China